Home Labaru Ilimi Gwamnatin Najeriya Ta Ayyana Litinin Ranar Hutu

Gwamnatin Najeriya Ta Ayyana Litinin Ranar Hutu

1
0

Gwamnatin tarayya ta ayyana Litinin, 12 ga watan Yuni a
matsayin ranar hutu ga ma’aikata domin murnar bikin Ranar
Dimokraɗiyya.

Wata sanarwa daga Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta taya ‘yan Nijeriya murna, ta na mai cewa dimokraɗiyyar Nijeriya ta gamu da cikas da kuma nasara kamar a ko ina.

A shekara ta 2018 ne, tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya sauya ranar bikin dimokuraɗiyyar zuwa 12 ga watan Yuni na kowace shekara maimakon ranar 29 ga watan Mayu.

Buhari dai ya sauya ranar ne da zummar tunawa da marigayi MKO Abiola, wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na ranar 12 ga watan Yunin shekara ta 1993, amma gwamnatin soji ta soke sakamakon sa.