Gwamnan jihar Kwara Abdulrahman Abdulrazaq, ya amince
da wani shirin bada tallafi na biliyoyin naira ga ma’aikatan
jihar, domin rage masu radadin cire tallafin man fetur da aka
yi a baya-bayan nan.
Tallafin, wanda babban sakataren yada labarai na gwamnan Rafiu Ajakaye ya kaddamar a wani taron manema labarai a Ilorin, an raba shi sassa daban-daban da ke karkashin gwamnati a fadin jihar.
Tare da tallafin dai, akwai tallafin kudi na Naira dubu 10 ga kowane ma’aikacin gwamnati, wanda za a fara kaddamar da shi a wannan watan, kuma zai cigaba har sai an bullo da shirin sabon mafi karancin albashi.
Ajakaye, ya ce an dauki matakin ne domin rage wa ma’aikata kalubalen da su ke fuskanta a kan tabarbarewar tattalin arziki da cire tallafin man fetur ya haifar a fadin Nijeriya.