Home Labaru Gwamnatin Kano Ta Musanta Cewa Ta Na Shirin Sauke Sarki Sunusi II

Gwamnatin Kano Ta Musanta Cewa Ta Na Shirin Sauke Sarki Sunusi II

359
0

Gwamnatin jihar Kano ta musanta zargin da wata kungiya ta yi cewa, ta na shirin sauke Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na II a karagar mulki.

kungiya mai suna The Renaissance Coalition a turance, ta yi zargin cewa, gwamnatin Kano ta shirya maida Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II zuwa masarautar Bichi.

Kakakin kungiyar Ibrahim Waiya, ya ce a karkashin shirin, da zarar Sarki Sanusi ya ki amincewa da sauyin da za a yi mashi, gwamnatin za ta yi amfani da damar wajen sauke shi daga karagar mulki.

A karshe kungiyar ta bukaci gwamnatin tarayya da masu fada aji, su gaggauta sa baki wajen jan hankalin gwamnan Abdullahi Umar Ganduje domin ya kauce wa abin da zai haifar da tashin hankali a jihar baki daya.