Home Labarai Gwamnatin Anambra Ta Yafe Wa Masu Ƙananan Sana’o’i Haraji

Gwamnatin Anambra Ta Yafe Wa Masu Ƙananan Sana’o’i Haraji

27
0
Mefor 1
Mefor 1

Gwamnatin jihar Anambra ta cire masu ƙananan sana’o’i da jarin su yake ƙasa da Naira dubu100 daga biyan haraji.

Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Law Mefor, ne ya bayyana haka a wata sanarwa, inda ya ce gwamnatin ta zartar da hakan ne a ƙarshen taron majalisar zartarwar jihar karo na 37.

Mefor ya jaddada cewa dokar yaƙi da zaman-banza da kashe wando da yawon tasha ta jihar har yanzu tana nan da ƙarfin ta,

Don haka ya shawarci matasa su shiga shirin koyar da sana’o’i da bayar da jari na gwamnatin jihar domin cin gumin su ta halaliya.

Kwamishinan ya kuma yi kira ga masu zuba jari su karɓi kamfanonin gwamnati na jihar, inda yake cewa bayar da su haya ko jinginar da su ga ‘yan kasuwa ya fi a ce gwamnati na tafiyar da su.

Leave a Reply