Home Labaru Ilimi Gwamnati Za Ta Dakatar Da Ɗaukar Nauyin WAEC Da Sauransu

Gwamnati Za Ta Dakatar Da Ɗaukar Nauyin WAEC Da Sauransu

276
0

Gwamnatin Tarayya, ta ce ba za a cigaba da ware wa
hukumomi da majalisun ƙwararru kaso daga asusun gwamnati
ba ba kamar yadda aka saba, kuma matakin zai fara aiki ne
daga ranar 1 ga Janairu na shekara ta 2024.

Babban Daraktan Ofishin Kasafi Ben Akabueze ya bayyana haka a cikin wata wasiƙar da ya aike wa hukumomi da cibiyoyin da lamarin ya shafa.

Wasiƙar dai ta nuna cewa, an ɗauki matakin ne daidai da shawarar Kwamitin Shugaban Ƙasa a Kan Albashi.

Da dama ‘yan Nijeriya na da ra’ayin cewa matakin da gwamnatin ta ɗauka ba ya rasa nasaba da ƙoƙarin da gwamnati ke yi na rage kuɗaɗen da ta ke kashewa.

Alamu na nuni da cewa, matakin zai shafi har da batun jarrabawar kammala sakandare ta WAEC da gwamnati ta saba ɗaukar nauyi.

Leave a Reply