Home Home Gwamnati Na Aiki Tukuru Don Rage Radadin Tsadar MAN FETUR – Akume

Gwamnati Na Aiki Tukuru Don Rage Radadin Tsadar MAN FETUR – Akume

121
0

Sakataren gwamnatin tarayya George Akume ya ba ‘yan Nijeriya tabbacin cewa, gwamnatin ta na aiki tukuru wajen samar da shirye-shirye da za su rage musu radadin tsadar farashin man fetur da ake fama da ita.

Tun bayan cire tallafin main fetur dai, ana kuma ci-gaba da samun karin hauhawar farashin kayan masarufi a daukacin fadin Nijeriya.

‘Yan Nijeriya da dama sun soki wannan matakin da gwamnatin tarayya ta dauka, amma George Akume ya ce gwamnati na kan daukar matakan da za ta rage wa ‘yan Nijeriya radadin da su ke ji na hauhawar farashin kayan masarufi. Sakatare ya bayyana haka ne a shafin sa na Twitter, inda ya ce gwamnati ta ji koke-koken da ‘yan Nijeriya ke yi, kuma ta na kan aiki domin lalubo mafita a kan lamarin, don haka ya roki ‘yan Nijeriya su cigaba da hakuri.

Leave a Reply