Ministan Harkokin Kuɗaɗe,ya ce Gwamnatin Tarayya ba ta da wata aniyar kamfatar kuɗaɗen Asusun Ajiyar ‘Yan Fansho,
Gwamnatin tarayya ta bayyana shiri ko tunanin da take yi na yiwuwar kamfatar kuɗaɗe daga Asusun ‘Yan Fansho, domin wasu ayyukan
Wannan furuci ya haifar da cece-kuce da suke kan gwamnatin Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu,
kuma da yawa na tunanin makomar kuɗaɗen da ma’aikata suka shafe shekara da shekaru su na tarawa.
Wole Edun ya ce hukumar fansho ta na tattare da tsauraran dokoki da sharuɗɗan da ba za a iya amfani da kuɗaɗen ta,
kuma ma gwamnati ba ta da niyyar karya waɗannan sharuɗɗa ko dokoki har ta kamfaci kuɗaɗen.
Ya ce sanarwar aka yi kan wannan batu a zaman Majalisar Zartarwa, tashin-zance ne kawai,
amma ba a ma nemi amincewa a cire kuɗaɗen ballantana har a riƙa surutai cewa za a cire.
An yi tashin zancen ne domin samar da hanyoyin kare tsarin ajiyar kuɗaɗe na dogon zango,