Home Labaru Gwamnan Zamfara Ya Buƙaci A Maida Hanyar Funtua-Gusau Ta Zama Tagwaye

Gwamnan Zamfara Ya Buƙaci A Maida Hanyar Funtua-Gusau Ta Zama Tagwaye

345
0

Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara, ya yi kira ga
Gwamnatin Tarayya ta samar da tagwayen hanyoyi daga
Gusau zuwa Funtua domin bunƙasa ci-gaban jihar.

Bayanin hakan, ya na ƙunshe ne a cikin sanarwar da mai magana da yawun Gwamnan Nuhu Salihu ya fitar a Gusau.

Gwamna Dauda Lawal ya yi kiran ne, a lokacin da ya kai wa Babban Sakataren Ma’aikatar Ayyuka ta Tarayya Mamuda Mamman ziyarar aiki a ofishin sa, inda ya ce hakan wani ɓangare ne na alƙawurran da ya yi wa talakawan sa lokacin yakin neman zaɓe.

Ya ce maida hanyar ta zama tagwaye aiki ne mai muhimmancin da zai bunƙasa harkokin tattalin arziki a jihar Zamfara, kuma a shirye jihar ta ke domin yin haɗaka da Gwamnatin Tarayya wajen aiwatar da ayyukan ci-gaba a faɗin jihar Zamfara.

A nasa ɓangaren, Mamuda Mamman ya ba Gwamnan tabbacin cewa, a shirye ma’aikatar ta ke ta haɗa hannu da Gwamnatin Zamfara a fannin gina hanyoyi domin samar da muhimmin ci- a jihar.

Leave a Reply