Home Labarai Gwamnan Ya Bada Tallafin Motoci Da Babura Ga Hukumomi

Gwamnan Ya Bada Tallafin Motoci Da Babura Ga Hukumomi

278
0
Uba Sani (1)
Uba Sani (1)

Sanata Uba Sani ya kaddamar da motoci da babura da aka rabawa jami’an tsaro wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma jihar.


Gwamna Uba Sani a yayin taron, ya bayyana cewa, ya fahimci kalubalen da jami’an tsaron ke fuskanta a jihar,

musamman ta fannin zirga-zirga da kuma saurin kai dauki lungu da sako, ya kuma sake nanata kira a sake duba dokar kaddamar da
‘yansandan Jiha.


Da yake jinjinawa jami’an tsaron da suka rasa rayukan su a kokarin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a jihar,


saboda haka ya umarci ma’aikatar tsaron cikin gida da harkokin cikin gida ta sanya wa dakin taro na ma’aikatar sunan Laftanar
Kanar AH Ali,

wanda ya yi aiki tare da bayar da gudunmawa sosai wajen tabbatar da tsaro a Jihar Kaduna a lokacin da yake rike da mukamin kwamandan runduna ta musamman ta 198,


kafin daga bisani a mayar da shi yankin Kudu-maso-Kudu, inda shi da hafsoshi da sojojin sa suka rasa rayukan su.


A na sa bangaren, babban hafsan tsaro na kasa, Janar Chrispher Musa ya yabawa gwamnatin Jihar Kaduna bisa tallafin ababen hawa ga hukumomin tsaron.

Leave a Reply