Gwamnan Jihar Sokoto Ahmed Aliyun ya raba wa iyalan wadanda harin ’yan bindiga ya shafa a jihar gero, sannan ya bada tallafin kudi ga wadanda su ka samu rauni ko rasa wata kadara a lokacin harin.
A makon da ya gabata ne, ‘yan bindiga su ka kai hari a wasu kauyukka biyar da ke Karamar Hukumar Tangaza, inda su ka kashe mutane 37 yayin da wasu da dama su ka samu rauni.
Gwamna Ahmad Aliyu, ya ziyarci mutanen ne tare da rakiyar mataimakin sa Idris Muhammad Gobir, da Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar da jagoran jam’iyar APC na jihar Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, wanda ya bayyana harin a matsayin na rashin hankali da dakikanci.
Haka kuma, gwamnan ya ba mutanen jihar Sokoto tabbacin cewa gwamnati ba za ta huta ba har sai ta kare rayuwar al’umma da dukiyoyin su.