Home Home Gwamnan Jihar Abia Ya Dakatar Da Karɓar Haraji Daga Masu Motocin Haya...

Gwamnan Jihar Abia Ya Dakatar Da Karɓar Haraji Daga Masu Motocin Haya Da Babura

440
0

Gwaman jihar Abia ya dakatar da karbar duk wani haraji daga direbobin motoci da Babura samfurin Keke NAPEP na haya a fadin jihar.

Umarnin Gwamna dai ya ya na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman ta fuskar yada labarai Ferdinand Ekeoma ya fitar.

Ya ce umarnin ya na daga cikin alkawarin da gwamnan ya dauka a lokacin yakin neman zabe na gyara tsrain karbar haraji a jihar, domin kawo karshen yadda ake muzgunawa da kuma tatsar masu motoci kudade.

Umarnin ya shafi dukk wani haraji da ake karba da sunan gwamnatin jiha daga masu motoci da sauran ababen hawa da ke jihar.

Gwamnatin jihar Abia, ta ce tsarin da ake amfani da shi wajen karbar harajin tsohon yayi ne, wanda ya ke cutar da rayuwar al’umma da tattalin arzikin jihar, don haka ta ce a dakatar da shi har sai ta sake yin nazari.

Leave a Reply