Home Labaru Gwamnan Gombe Ya Nada Njodi Sakataren Gwamnati, Misilli Daraktan Yada Labarai

Gwamnan Gombe Ya Nada Njodi Sakataren Gwamnati, Misilli Daraktan Yada Labarai

101
0

Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya, ya
amince da nadin Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi a matsayin
Sakataren Gwamnatin jihar.

A cikin wata sanarwar da babban Sakataren fadar Gwamnatin jihar Gombe Barista Balarabe Poloma ya fitar, ya ce gwamna Inuwa ya kuma amince da nadin Ismaila Uba Misilli a matsayin darakta-janar na harkokin yada labarai da hulda da ‘yan jarida.

Haka kuma, gwamna Inuwa ya nada Dakta Mu’azu Shehu a matsayin darakta-janar na Sashen bincike da taskace bayanai.

Sanarwar ta kara da cewa, dukka nade-naden sun fara aiki ne tun daga ranar 1 ga watan Yuni na shekara ta 2023.

Leave a Reply