Home Home Gwamna Ya Tona Yadda Tsohon Gwamnan APC Ya Sulale Da Motoci 17...

Gwamna Ya Tona Yadda Tsohon Gwamnan APC Ya Sulale Da Motoci 17 Da Kayan OFIS

81
0

Sabon gwamnan jihar Zamfara Dakta Dauda Lawal Dare, ya zargi Bello Muhammad Matawalle da barin gidan gwamnatin jihar da kayan al’umma.

Rahotanni sun Ambato Dauda Lawal Dare ya na cewa, Bello Matawalle ya dauke motoci da kayan aiki lokacin da zai bar ofis, ya na mai babu abin da ya gada a baitul-malin jihar Zamfara illa tarin bashi.

Ya ce kafin Gwamna Matawalle ya bar ofis, sai da ya tattara motoci 17 da ake da su a ofishin Gwamna da ofishin Mataimakin Gwamna.

Gwamna Lawal ya kara da cewa, ya iske an yi gaba da talabijin da na’urar dafa abinci da ta sanyaya daki da firiji daga gidan gwamnati kafin a rantsar da shi.

Ya ce ta’adin da aka tafka ya wuce tunani don ban taba ganin rashin sanin ya kamata irin wannan ba, ya na mai ba al’ummar jihar Zamfara tabbacin cewa  za su yi bakin kokarin su wajen gyara kura-kuran da aka tafka.

Leave a Reply