Home Home Gwamna Raɗɗa Zai Sake Fasalta Hukumar Tattara Kuɗaɗen Haraji Ta Jihar Katsina

Gwamna Raɗɗa Zai Sake Fasalta Hukumar Tattara Kuɗaɗen Haraji Ta Jihar Katsina

101
0

Gwamnan Jihar Katsina Dikko Umaru Raɗɗa, ya shirya sake fasalta Hukumar Tattara Kuɗaɗen Haraji ta jihar domin bunkasa hanyoyin samar da kuɗaɗen shiga.

Dikko Radda ya sanar da haka ne, lokacin wani taron gaugawa da ya kira hukumomin da ke samar da kuɗaɗen shiga a gidan gwamnatin jihar Katsina.

Gwamna Raɗɗa, ya ce babban maƙasudin taron shi ne, domin a ƙara faɗakar da hukumomin da ke samar da kuɗaɗen shiga su kara matsa kaimi wajen gudanar da ayyukan su don tattalin arzikin jihar Katsina ya bunƙasa.

Dikko Umar Raɗɗa, ya kuma koka da yadda ake samun ƙarancin bin doka wajen biyan kuɗaɗen haraji, da kuma halayyar wasu jami’an tattara kuɗaɗen haraji da ya ce hakan ya na a sahun gaba wajen taimakawa ana samun nakasu ta fuskar tattara kuɗaɗen shiga.

Ya ce kudirin sa shi ne, jihar Katsina ta rika samar da kudaden da za ta biya albashin ma’aikata ba sai ta jira dauni daga gwamnatin tarayya ba, inda a ƙarshe ya buƙaci Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina Ahmad Musa Ɗangiwa ya kafa kwamitin musamman, wanda zai yi nazari a kan yadda ake samun kuɗaɗen shiga a wasu jihohin da ke samun kuɗaɗe da yawa domin Katsina ta kwaikwaye su.

Leave a Reply