Gwamna Darius Ishaku na Jihar Taraba, ya sa hannun
amincewa a kamfaci naira biliyan 2 domin a sayo ma shi da
matar sa da mataimakin sa da matar mataimakin sa motocin
alfarma.
Za a kamfaci kuɗaɗen a sayo masu motocin bankwana da talakawan jihar ne, makonni biyu kafin fitar su daga gidan gwamnatin Taraba.
Gwamna Ishaku da mataimakin sa daiza su kammala wa’adin su na shekaru takwas a kan mulki a ranar 29 Ga watan Mayu.
Motocin da za sayo wa Gwamna dai sun hada da Land Cruiser Toyota SUV guda biyu, da Toyota Hilux biyu wadda jami’an tsaron sa za su riƙa yi ma shi rakiya a cikin ta, da kuma wata rangaɗeɗiyar mota ɗaya, yayin da za a sayo wa matar sa Toyota Land Cruiser SUV ɗaya da motar jami’an tsaro ɗaya.
An dai amince a cire kuɗin a sayo motocin ne lokacin Taron Majalisar Zartarwa ta Jihar na Ƙarshe.














































