Home Labarai Garkuwa Da Mutane: ‘Ƴan Bindiga Sun Sace Basarake A Yankin Kubuwa Dake Abuja

Garkuwa Da Mutane: ‘Ƴan Bindiga Sun Sace Basarake A Yankin Kubuwa Dake Abuja

21
0

‘Yan bindiga sun sace mai Anguwar Kuchibiyu da ke Kubwa, ƙaramar hukumar Bwari a babban birnin tarayya Abuja.

Wata majiya a unguwar ta ce an sace Malam Isiaka Dauda ne a cikin gidansa, yayin harin wanda aka fara kai wa tun daga sha biyu na dare zuwa daya na dare.


Majiyar tace ƴan bidigar da yawansu ya kai goma, sun yi harbi sau biyu bayan zuwansu, abun da ya jefa fargaba a zukatan mutanen.


Ya zuwa yanzu dai masu garkuwar ba su buƙaci komai ba tukuna.

Babban jami’in ƴan sandan yankin Kubwa ACP Muhammad Ndagi wanda ya tabbatar da lamarin ya ce za su gudanar da bincike.

Wannan na faruwa ne watanni uku bayan Garkuwa da mai Anguwar Bukle da ke yankin Kwali a yankin babban Birnin tarayya Abujan Alhaji Hassan Shamisozhi a fadarsa.