Home Home Gargadi: Shugaba Buhari Ya Yi Magana A Kan Rikicin Shugabancin APC

Gargadi: Shugaba Buhari Ya Yi Magana A Kan Rikicin Shugabancin APC

449
0
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya yi tsokaci a kan rikicin shugabanci da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa a jam’iyyar APC.

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya yi tsokaci a kan rikicin shugabanci da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa a jam’iyyar APC.

A cikin wata sanarwa da kakakin sa Garba Shehu ya wallafa a shafin sa na Facebook, shugaba Buhari ya gargaɗi jagororin jam’iyyar su guji kiran suna da cin dudduniyar junan su.

Shugaba Buhari ya kara jaddada cewa, babban ganganmin jam’iyyar APC na ƙasa ya na nan daram a ranar 26 ga watan Maris na shekara ta 2022.

Buhari ya roki ‘yan jam’iyyar APC su kauda duk wani saɓani da ke tsakanin su, su kuma haɗa kai matukar su na son jam’iyyar ta cigaba da samun nasara a dukkan matakai.

LEAVE A REPLY