Shugaban Hukumar FA ta ce babu wani abin ta da hankali cikin kare matakinta na goyon bayan buƙatar Saudiyya na karɓar baƙuncin Kofin Duniya na 2034
Hukumar kwallon ƙafa ta duniya Fifa ce ta tabbatar da amince wa Saudiyya ta karɓi baƙuncin gasar a ranar Laraba.
Wadanda za su shirya gasar sun ce suna maraba da kowa, sai dai ana ta sukar ƙasar da take haƙƙin ɗan adam, mata da kuma nuna wariya ga masu auren jinsi.
Hewitt ta shaida wa BBC cewa FA ta yi tambayoyi masu yawa gabanin amincewa da buƙatar Saudiyya.
FA ta zauna da hukumar kwallon ƙafa ta Saudiyya domin tattaunawa ɗaya bayan ɗaya kan buƙatarta ta neman karɓar baƙuncin.
Hukumar Kwallo Kafa ta Saudiyya ta tabbatar da cewa za ta samar da yanayi mai kyau ga duk wani baƙo da zai je kallon wasan – ciki har da magoya baya masu ra’ayin LGBTQ.