Home Labarai Fidda-Gwani: APC Ta Kawar Da Batun Maslaha A Tsaida Dan Takarar Shugaban Kasa

Fidda-Gwani: APC Ta Kawar Da Batun Maslaha A Tsaida Dan Takarar Shugaban Kasa

85
0

Jam’iyyar APC ta ce ba za a yi maslaha wajen zaben fitar da
gwani na ‘yan takarar shugaban kasa ba.

APC ta bayyana haka ne, a yayin taron majalisar zartarwar ta a
karkashin jagorancin Shugaba Buhari, wanda shugabannin
jam’iyyar na kasa da jihohi da gwamnoni da sauran jiga-jigan ta
daga sassan Nijeriya su ka halarta.

Jam’iyyar APC ta sanar da saida Fom na takarar shugaban ƙasa
a kan naira miliyan 100.

Wani jadawalin gudanar da zaɓubbukan fidda gwani da
jam’iyyar ta fitar ya nuna cewa, masu son yin takarar shugaban
ƙasa a ƙarƙashin tutar APC za su biya kuɗin na-gani-ina-so naira
miliyan 30, sai kuma kuɗin Fom naira miliyan 70.

Hakja kuma, masu son yin takarar gwamna za su lale naira
miliyan 50, yayin da sanatoci za su biya naira miliyan 20, yayin
da masu neman kujerar ‘yan majalisar wakilai za su biya naira
miliyan 10, sai kuma ‘yan majalisar jiha da za su biya naira
miliyan biyu.