Hukumar bada agajin gaugawa ta birnin Tarayya Abuja FEMA, ta yi gargaɗin samun ruwan sama mai karfin gaske, wanda zai iya haifar da ambaliya a birnin Abuja da wasu jihohi a ranakun Asabar da Lahadi.
A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ɗauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na hukumar Nkechi Isa, ya ce hukumar ta na gargaɗin ne bayan hukumar kula da yanayi ta ƙasa ta yi hasashen samun ruwan sama mai ƙarfin haɗe da iska da ambaliya da zaizayewar ƙasa a wasu sassan jihohin Katsina da Kano da Bauci da Filato da Taraba da kuma Abuja.
Hukumar kula da yanayi ta kasa NiMET dai ta yi hasashen cewa, za a samu ambaliyar ruwa tare da batsewar koguna da iska mai ƙarfi da zaizaiyewar ƙasa da walkiya da kuma tsawa.
Haka kuma, Hukumar ta yi kira da a sauya matsugunai ga al’umomin da ke cikin hatsarin fuskantar ambaliyar, wadda za ta iya lalata dukiyoyi tare da haifar da cutattuka.
Babban daraktan hukumar bada agajin gaugawa na birnin Abuja Dakta Abbas Idriss, ya ce hukumar ta sa jami’an ta cikin shirin ko-ta-kwana domin fuskantar matsalar, sannan ya yi kira ga mazauna birnin Abujasu riƙa la’akari da gargadin da hukumar ta fitar, tare da kauce wa yin tuƙi ko tafiya a ƙafa lokacin da ake tsaka da ruwan sama, tare da kauce wa titunan da ruwan zai iya mamayewa.