Home Labarai Fastocin Ƙarya Ne Suka Halarci Taron Ƙaddamar Da Shettima – Inji CAN

Fastocin Ƙarya Ne Suka Halarci Taron Ƙaddamar Da Shettima – Inji CAN

161
0

Kungiyar Kiristoci ta Nijeriya, CAN, ta ce duk Fastocin su ka halarci taron kaddamar Kashim Shettima a helkwatar jam’iyyar APC da ke Abuja na bogi ne.

Kakakin kungiyar Bayo Oladeji, ya ce duk waɗanda aka gani a wurin taron sanye da dogayen riguna a wurin duk ba fastocin kwarai ba ne.

An dai ƙaddamar tsohon gwamnan jihar Barno Kashim Shettima a matsayin mataimakin ɗan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC Bola Ahmen Tinubu a Abuja, inda a wurin taron aka ga wasu da dama sanye da kayan limaman coci-coci.

Hakan ya jawo cece-kuce musamman kafafen yaɗa labarai na yanar gizo, inda wasu da dama ke la’antar waɗannan fastoci, yayin da Oladeji ya ce su dai kiristoci ba su tare da tafiyar Tinubu da ya zaɓi musulmi a matsayin mataimaki.