Home Labarai Fasahar Zamani: Inec Ta Ce Kutse a Na’urar Tattara Sakamakon Zabe Ya...

Fasahar Zamani: Inec Ta Ce Kutse a Na’urar Tattara Sakamakon Zabe Ya Kare a Najeriya

229
0

Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta kara tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa ba za a iya yin kutse domin sauya bayanan da ke cikin na’urorin tattara sakamakon zabe ba a yanzun.

Babban mataimakin shugaban hukumar mai kula da sashen fasahar zamani Lawrence Bayode, ya tabbatar da haka a lokacin da yake amsa tambayoyi a wani shiri na gidan Talbijin na Channels.

Ya ce yana so ya sake tabbatar da cewa an yi duk abin da ya kamata wajen kiyaye duk bayanan da ke cikin na’urar.

Ya ce bayan zaben, idan za a turo da bayanan zuwa babbar na’ura, za a kiyaye bayanan a lokacin da ake turo su, sannan bayan sun zo babbar na’urar, za a ci gaba da lura tare da kiyaye su.

Ya kara da cewa hukumar zaben ta tsaurara matakai domin tabbatar da cewa ba a yi wa na’urorin kutse  ba.

Leave a Reply