Home Home Fargabar Rashin Tsaro: Ana Safarar Makaman Yakin Rasha Da Ukraine Zuwa Yankin...

Fargabar Rashin Tsaro: Ana Safarar Makaman Yakin Rasha Da Ukraine Zuwa Yankin Tafkin Chadi-Buhari

35
0

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi zargin cewa ana safarar wasu daga cikin makaman da ake fafata yaki tsakanin Rasha da Ukraine zuwa yankin Tafkin Chadi.

Buhari ya furta haka ne, lokacin da yake jawabi yayin bude taron Shugabannin Kasashen Hukumar Raya Tafkin Chadi (LCBC), karo na 16 a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.

Taron ya sami halartar dukkan shugabannin kasashe shida na yankin, in ban da Paul Biya na Kamaru, wanda daya daga cikin Ministocinsa ya wakilta.

Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da Shugaban Jamhuriyyar Afirka ya Tsakiya, Farfesa Faustine Archange Touadera da na Nijar, Mohamed Bazoum da na Benin, Patrice Tallon da Shugaban rikon kwarya na Chadi, Mahamat Idriss Deby Itno, da kuma Shugaban mulkin soja na Libya, Mohamed Al- Menfi.

Shugaba Buhari, wanda kuma shi ne shugaban taron, ya ce lamarin, wanda ya kara yaduwar kanana da matsakaitan makamai a yankin, abin damuwa ne.

Buhari ya kuma ce shigowar makaman na yakin Rasha da Ukraine ya dada ta’azzara rikicin Boko Haram da na ta’addanci a yankin.