Home Labaru Kasuwanci Farashin Litar Man Dizel Ka Iya Haura Naira Dubu Guda A Nijeriya

Farashin Litar Man Dizel Ka Iya Haura Naira Dubu Guda A Nijeriya

74
0

Kungiyar masu safarar mai da iskar gas ta Najeriya, ta yi hasashen cewa nan ba da jimawa ba farashin Man Dizel zai iya kaiwa naira dubu daya da dari biyar.

Wannan gargadin dai ya zo ne, yayin da farashin litar Man Dizal a Nijeriyar ya kai naira 800.

Tuni dai hasashen ya jefa ‘yan Nijeriya da dama cikin zullumi, duba da halin da ake ciki na matsin rayuwa sakamakon yadda farashin kayayyakin da ake sarrafawa a masana’antu su ka yi tashin gauron zabo.

Yanzu haka dai, galibin gidajen man Nijeriya sun daina saida Man Dizel saboda tsadar da ya yi, duk kuwa da cewa da shi ne ake safarar Man Fetur zuwa sassan kasar nan.

Shugaban kungiyar masu safarar mai da iskar gas ta Nijeriya Bannet Korie, yay i gargadin cewa matsawar aka cigaba da tafiya a haka ba tare da daukar kwararan matakai ba lallai farashin zai iya kaiwa naira dubu 1 da 500.