Home Home Fallasa: Majalisa Na Binciken Bashin Tiriliyan 2.6 Da Gwamnati Ke Bin Kamfanonin...

Fallasa: Majalisa Na Binciken Bashin Tiriliyan 2.6 Da Gwamnati Ke Bin Kamfanonin Mai

365
0

Majalisar Wakilai ta ƙaddamar da bincike a kan kuɗi sama da naira tiriliyan biyu da rabi da gwamnatin tarayya ke bin kamfanonin man fetur 77 bashi.

Wata majiya ta ce, ‘yan majalisar su na aiki ne da wani rahoton shekara ta 2019 da kwamatin tabbatar adalci a bangaren masana’antu na Nijeriya ya gabatar.

Kakakin Majalisar wakilai Femi Gbajabiamila ya yi barazanar cewa, majalisar za ta yi amfani da tanadin kundin tsarin mulki a kan duk kamfanin da ya ƙi ba binciken da su ke yi haɗin kai.

Gbajabiamila ya kara da bada tabbacin cewa, idan aka samu wani mutum ko kamfanin da ya ƙi ba binciken da su key i haɗin kai, zai zama lokaci na farko da majalisa ko kuma shi zai yi amfani da ikon kundin tsarin mulki a kama shi. Kakakin majalisar ya ƙara da cewa, naira tiriliyan 2 da biliyan 600 bai kamata a ƙyale su tafi a banza ba.

Leave a Reply