Home Labaru Kasuwanci Fadiwar Farashi: OPEC Ta Yi Taro Domin Duba Yiwuwar Rage Yawan Man...

Fadiwar Farashi: OPEC Ta Yi Taro Domin Duba Yiwuwar Rage Yawan Man Da Take Fitarwa

87
0

Ƙungiyar ƙasashe Masu Arzikin Man Fetur ta OPEC ta gudanar da taro a jiya Lahadi tare da ƙawayen ta domin tattauna batun rage yawan man da ƙungiyar ke fitarawa zuwa kasuwannin duniya.

OPEC ta shirya taron ne a daidai lokacin da farashin man ke faɗuwa a kasuwannin duniya sakamon matsin tattalin arziki da mafiya yawan ƙasashen duniya ke fuskanta, lamarin da ya haifar da rage yawan buƙatar man a ƙasashen.

Ministocin ƙasashe ‘yan ƙungiyar 13 tare da ƙawayen ta da Rasha sun gana a shalkwatar ƙungiyar da ke birnin Vienna domin tattaunawa game da batun.

A watan Afrilun da ya gabata ne ƙungiyar ta rage adadin man da take fitarwa zuwa kasuwannin duniya a wani mataki na farfado da farashin man a kasuwannain duniya.

Leave a Reply