Home Labaru Ilimi El-Rufai Ya Kekketa Rigar Mutuncin Gwamnatin Tarayya A Gaba Ɗaliban Kwalejin Malali

El-Rufai Ya Kekketa Rigar Mutuncin Gwamnatin Tarayya A Gaba Ɗaliban Kwalejin Malali

1
0

Zazzafan rikici ya ɓarke tsakanin Gwamnatin Tarayya da
Gwamna Nasiru El-Rufa’i na jihar Kaduna, sakamakon zargin
da gwamnatin tarayya ta yi cewa gwamnatin Kaduna ta yi cin-
iyaka, inda ta shiga filin Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke
Malali a garin Kaduna.

Duk da cewa saura kwanaki 19 El-Rufa’i ya sauka daga mulkin jihar Kaduna, Ma’aikatar Ilmi ta Tarayya ta garzaya kotu, inda ta samo sammacin umarnin hanawa ko dakatar da gwamnatin jihar Kaduna ci-gaba da gine-gine a cikin filin kwalejin.

Tun a ranar 2 ga watan Mayu ne, Mai Shari’a B.F Zubairu na Babbar Kotun Kaduna ya karbi roƙon Ma’aikatar Ilmi ta Tarayya, inda ya umarci Gwamnatin Jihar Kaduna ta daina shiga ko yin gine-gine ko gilmawa ta cikin filin mallakar Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Malali.

Bayan Ma’aikatar Ilmi ta samu umarnin da ta ke nema a kotu, sai ta rubuta wasiƙa zuwa ga shugaban ‘yan sandan Nijeriya Usman Alƙali Baba, inda ta nemi ya tura zaratan ‘yan sanda domin su hana gwamnatin Kaduna ci-gaba da gine-gine a cikin filin kwalejin.

Babban Sakataren Ma’aikatar Ilmi Andrew Adejo ya rubuta wasiƙar. domin a kare ƙananan yara da dukiya da kadarorin kwalejin.