Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC, ta ce za ta ɗaukaka ƙara a kan hukuncin da wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke, na wanke tsohon shugaban ma’aikata na ƙasa daga zargin halasta kuɗin haram kimanin naira biliyan biyu da hukumar ke yi ma sa shi da wasu.
A wani saƙo da hukumar ta wallafa a shafin ta na Facebook, EFCC ta ce za ta ƙalubalancin hukuncin a gaban kotun ɗaukaka ƙara.
EFCC dai ta na zargin Steve Oronsaye da mutunen da ake zargin su tare da yin amfani da wasu kamfanoni wajen karkatar da kuɗin gwamnati ta hanyar amfani da kwangilolin bogi.
Yayin da ya ke watsi da ƙarar, alƙalin kotun mai shari’a Inyang Ekwo ya ce hukumar EFCC ta kasa tabbatar da zarge-zargen da ta ke yi wa Oronsaye.
Sai dai a cikin sanarwar da mai magana da yawun hukumar Wilson Uwujaren ya fitar, ya ce alƙalin ya yi kuskure, saboda bai yi la’akari da shaidun da masu ƙara su ka gabatar ba a tsawon shari’ar, tare da bahasin da ɗaya daga cikin waɗanda ake ƙarar Osarenkhoe Afe ya furta da bakin sa a gaban kotun.