Home Labaru EFCC Ta Kama Manaja A Kan Karkatar Da Kuɗaɗen Mahajjata

EFCC Ta Kama Manaja A Kan Karkatar Da Kuɗaɗen Mahajjata

160
0

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC, ta tsare Dataktan kamfanin jirgin sama na Medview Airline Muneer Bankole bisa zargin karkatar da kuɗin aikin Hajji.

Wata majiya da ke da alaƙa da lamarin, ta ce hukumar EFCC ta gayyaci Bankole ne bisa zargin karkatar da kashi 50 cikin 100 na kuɗaɗen da aka ba shi.

Hukumar EFCC dai, ta na zargin shugabam kamfanin jiragen saman ne da karkatar da kuɗaɗen da hukumar aikin Hajji ta ƙasa ta ba shi domin gudanar da aiki.

Majiyar ta kara da cewa, ana zargin Bankole da wasu ƙarin Dala dubu 900 da aka ba shi domin jigilar mahajjata a shekara ta 2019.

Kakakin hukumar EFCC Wilson Uwujaren ya tabbatar wa manema labarai kama Muneer Bankole da aka yi.