Hukumar Yaki da cin hanci da rashawa EFCC ta gurfanar da
tsohuwar ministar sufurin jiragen sama ta Nijeriya Stella
Oduah, tare da wasu mutane takwas a gaban babbar kotun
tarayya da ke Abuja bisa zargin almundahanar kuɗaɗe.
An dai gurfanar da mutanen ne a kan zarge-zarge 25, wadanda su ka haɗa da halasta kuɗin haram da haɗin baki da amfani da wani asusun ajiyar banki maras suna a bankin First Bank da aka samu kimanin naira biliyan biyar a cikin sa.
Sai dai bayan an karanto zarge-zargen Stella Oduah tare da sauran mutanen ciki har da wata tsohuwar hadimar ta sun musanta duk zarge-zargen da hukumar ke yi masu.
Alkalin kotun Mai shari’a Inyang Ekwo, ya umarci ofishin Atoni-Janar na ƙasa ya karbi hurumin shigar da ƙarar daga hannun hukumar EFCC.














































