Home Labaru EFCC Ba Ta Taɓa Gayyata Ta Ba – Jonathan

EFCC Ba Ta Taɓa Gayyata Ta Ba – Jonathan

326
0

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya musanta
iƙirarin da mawaƙi Femi Kuti ya yi a kan sa cewa Hukumar
EFCC ta gayyace shi a kan zargin sha’anin kuɗi bayan wa’adin
sa ya ƙare a matsayin mataimakin gwamnan Jihar Bayelsa.

A baya-bayan nan ne, mawaƙin ya Jonathan ya taɓa zuwa hukumar EFCC a matsayin wanda aka yi wa tambayoyi ko gudanar da bincike a kan sa, sai dai wata sanarwa da tsohon shugaban kasar ya fitar ta musanta hakan.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne, jami’in yaɗa labarai ne a ofishin Goodluck Jonathan Wealth Dickson Ominabo ya fitar da sanarwar da ta ƙaryata wannan iƙirari.

Wealth Dickson, ya ce ya yi amfani da wasu bayanai da wasu su ka riƙa yaɗawa a baya a kan Jonathan domin su ɓata ma shi suna, inda su ka riƙa cewa sai da ya je hukumar EFCC domin amsa tambayoyi.

Leave a Reply