Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya jaddada cewa duk da ƙalubalen da tattalin arzikin duniya ke fuskanta da rigingimun cikin ƙasa hakan bai hana tattalin Nijeriya bunƙasa da ci-gaba ba.
Yayin da ya ke jawabi a wajen taron ƙaddamar da Kwamitin Shugaban Ƙasa Mai Bada Shawara a kan Tattalin Arziki a Abuja, Buhari ya ce tattalin arzikin Nijeriya gaba ya ya ke yi ba baya ba.
Shugaba Buhari, ya ce annobar korona da yaƙin Ukraniya da Rasha da asarar ɗimbin ɗanyen man fetur sun haifar wa tattalin arzikin Nijeriya naƙasu.
Ya ce duniya ta yi fama da manyan ƙalubale a cikin shekaru ukun da ake ciki, tun daga kullen korona, wanda ya tsaida komai ya kuma haifar da tashin gwauron zabon farashin kayan abinci da na masarufi a duniya.
Buhari ya ce Gwamnatin shi za ta cigaba da inganta rayuwar al’umma musamman a ƙarƙashin Shirin Inganta Rayuwar Marasa Galihu.
You must log in to post a comment.