Home Labaru Dubu Ta Cika: ‘Yan Sanda Sun Kashe Fitaccen Mai Satar Mutane A...

Dubu Ta Cika: ‘Yan Sanda Sun Kashe Fitaccen Mai Satar Mutane A Jihar Kogi

42
0
An Kashe Mutane 2 Da Ke Yi Wa ‘Yan Bindiga Leken Asiri A Katsina
An Kashe Mutane 2 Da Ke Yi Wa ‘Yan Bindiga Leken Asiri A Katsina

Jami’an tsaron da ke karamar hukumar Olamaboro ta jihar Kogi, sun kashe wani gagararren mai garkuwa da mutane bayan wata musayar wuta da su ka yi.

Wata majiya ta ce, hatsabibin dan ta’addan ya taba sace mahaifin sa, kuma sai da ya karbi kudi naira miliyan hudu na fansa kafin ya sako shi.

Dan ta’addan dai yay i kaurin suna a garkuwa da mutane tare da fashi da makami, kuma jami’an tsaro sun dade su na neman shi amma sai a wannan lokacin dubun shi ta cika.

Haka kuma, wata tawagar hadin gwiwa ta jami’an tsaro bisa jagorancin shugaban karamar hukumar Olamaboro Adejohh Friday Nicodemus, sun kama wani mai suna Kizito Ocheme da ya shahara a bangaren satar mutane.