Sarkin Saudiyya Salman bin Abdul-aziz ya sa dokar hana zirga-zarga a daukacin kasar daga karfe 7 na dare zuwa 6 na safiyar kowanne rana na tsawon kwanaki 21 domin rage yaduwar cutar Corona.
Rahotanni daga kasar na cewa, Saudiyya ta fitar da sanarwar ne wacce za ta fara aiki ne daga ranar Litinin 23 ga watan Maris din nan.
Sanarwar ta kara da cewa, ma’aikatar kula da al’amuran cikin gida ce za ta tabbatar da dabbaka dokar, tare da hadin kan hukumomin Soji da ‘yan sanda da sauran hukumomin farin kaya.
Gwamnatin Sa’udiya dai, ta bukaci al’ummar kasar su zauna a gidajen su a lokacin dokar, kada wanda ya fito har sai ta kama, kamar domin duba lafiyar su da sauran su.
Sai dai, dokar ta daga kafa ga muhimman ma’aikatan gwamnati da na kamfanoni masu zaman kan su.
Daga
cikin wadanda dokar ta daga wa kafa, akwai jami’an tsaron sojoji da ‘yan jaridu da ma’aikatan lafiya da
jami’an ma’aikatun kudi da jami’an kamfanonin sadarwa da kuma jami’an hukumar ruwan
sha ta kasar.