Home Labaru Dikko Radda Ya Ba Alhazan Katsina Su 4,634 Kyautar Miliyan ₦278 A...

Dikko Radda Ya Ba Alhazan Katsina Su 4,634 Kyautar Miliyan ₦278 A Kasar Saudiyya

130
0

Gwamnan jihar Katsina Dikko Umar Radda, ya bada kyautar
Naira miliyan 278 ga Alhazan jihar Katsina a kasar Saudiyya.

Bayanin hakan ya fito ne a cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai a Katsina, ta hannun babban sakataren yada labarai na gwamnan Malam Ibrahim Kaula.

Ya ce Amirul Hajji na jihar kuma tsohon kakakin majalisar dokoki ta jihar Katsina Alhaji Tasiu Musa-Maigari ya bayyana hakan a Makkah lokacin da ya ziyarci maniyyatan.

Musa-Maigari ya kara da cewa, Dikko Radda ya kuma bukaci alhazai su yi addu’ar Allah ya kawo karshen rashin tsaro a jihar Katsina.

Leave a Reply