Kocin Leicester City Steve Cooper ya sanar da cewa ɗan wasan kungiyar na gefe Abdul Fatawu zai yi jinya zuwa ƙarshen kakar wasanni ta bana saboda raunin da ya ji a gwiwarsa.
Dan wasan mai shekara 20 ya ji raunin ne a lokacin da yake yi wa Ghana wasa, a wasan da suka yi da Angola yayin da ake wasannin ƙasashe.
Kocin ya ce abin babu dadi, mummunan rauni ya ji gashi Leicester City za ta karɓi baƙuncin Chelsea a Premier a ranar Asabar.
Danwasan ya ji rauni a gwiwar sa da ba zai bar shi ci gaba da buga wasanni ba har zuwa ƙarshen kakar nan.