Home Labaru Dambarwa: Rikici Ya Balle A Jam’iyyar Apc A Dai Dai Lokacin Da...

Dambarwa: Rikici Ya Balle A Jam’iyyar Apc A Dai Dai Lokacin Da a ke Fara Zaben Shugabanninta Na Mazaɓu

58
0

Sabon rikici na sake kunno kai a jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya kan halarcin shugabancin riko na jam’iyyar na kasa karkashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe yayin da za a fara zabukan shugabannin jam’iyyar na mazabu da kananan hukumomi.

Rikicin ya yi kamari ne sakamakon hukuncin da Kotun Koli ta yanke a ranar Laraba kan zaben gwamnan Jihar Ondo, wanda ya nuna shakku kan sahihancin Kwamitin shirya zabukan karkashin Gwamna Buni.

Hukuncin ya yi watsi da karar da dan takarar jam’iyyar PDP, a zaben gwamnan jihar Ondo na shekarar 2020, Eyitayo Jegede ya shigar, yana kalunbalantar nasarar Rotimi Akeredolu, na APC.

Karamin Ministan Kwadago da ayyuka na Najeriya, Festus Keyamo, ya gargadi jam’iyyar game da kyale Gwamna Buni ya jagoranci wadannan zabuka.

Sai dai jam`iyyar APC ta sake jaddada cewa hukuncin da kotun kolin ta yanke a kan shara`ar dan takarar gwamna na jam`iyyar PDP a jihar Ondo da gwamna Rotimi Akeredolu na jam`iyyar APC bai shafi halalcin shugabannin riko na jam`iyyar APC na kasa ba, kuma ba zai shafi ayyukan da suke aiwatarwa ba