Home Labaru Dalilin Da Ya Sa Nake Shiga Sha’Anin Gwamnatin Kano -Kwankwaso

Dalilin Da Ya Sa Nake Shiga Sha’Anin Gwamnatin Kano -Kwankwaso

293
0

Tsohon gwamnan Jihar Kano Sanata Rabiu Musa
Kwankwaso, ya bayyana dalilan da su ka sa har yanzu ya ke
tsoma baki a tafiyar da gwamnatin jihar.

Kwankwaso ya ce ya na tsoma bakin sa ne a tafiyar domin komai ya tafi yadda ya kamata a shugabancin jihar Kano kuma cikin tawaga daya.

Sanata Kwankwaso ya bayyana haka ne, yayin wata hira da gidan Rediyon Faransa, inda ya ce abin da mutanen jihar su ke son gani shi ne fara gudanar da aiki.

Ya ce duk bita da kullin da ‘yan adawa su ke yi don su karkatar da hankalin gwamnatin jihar Kano ba za su samu nasara ba, don haka Rusau da su ke yi a Kano gyara su ke yi, kuma wani abu ne da aka faro shi tun a shekara ta 2019, duk wani gwamna da ya yi gini a makaranta ko Masallaci ko ba za su lamunci hakan ba.

Leave a Reply