Gwamnatin jihar Sokoto ta ce ta tube wasu sarakunan
gargajiya 15 daga muƙamansu
Daga cikinsu kuma akwai shida da gwamnatin ta tube wadanda tsohuwar gwamnatin PDP ta nada, ta kuma sanar da mayar da wasu uwayen kasa da ta dakatar daga aiki kan kujerunsu.
Daga cikin wadanda ta tube su 15 akwai 9 da ta ce an tube su ne bayan zarginsu da hannu a matsalar tsaron jihar da kuma wawurar filaye da nuna rashin biyayya Gwamnatin ta ce ta dauki matakin tube su ne sakamako binciken da kwamitin da ta kafa ya gano kuma ta yi aiki da shawarwarin kwamitin.
Ya ce akwai wasu iyayen ƙasa da aka kuma sauya wa wuri, sai kuma wadansu da aka sauke.














































