Gwamnatin tarayya, ta ce daga yanzu ba za a rika daukar yara
‘yan kasa da shekaru 12 a makarantun sakandare na
gwamnatin tarayya ba, saboda a doka ba su kai su shiga
makarantar Sakandare ba.
Babban sakataren ma’aikatar ilimi Andrew Adejoh ya sanar da haka, yayin da ake sa Ido a jarabawar shiga makarantun sakandaren gwamnatin tarayya.
Adejoh, ya ce gwamnati a shirye ta ke domin ganin an kiyaye wannan doka, saboda yin hakan zai taimaka wajen kawar da matsalolin da fannin ilimi ke fama da su a Nijeriya.
Ya ce ya ga yaran da ba su wuce shekaru 10 ba, inda uku daga cikin su ‘yan shekaru 9 ne sun shiga makarantar sakandare.