Home Muryar 'Yanci Dalilan Da Su Ka Sa Amaechi Ya Yi Silar Cire Ni Daga...

Dalilan Da Su Ka Sa Amaechi Ya Yi Silar Cire Ni Daga Hukumar Npa – Hadiza Bala

80
0
Tsohuwar shugabar Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Nijeriya Hadiza Bala Usman ta fitar da wani littafi da ta wallafa, wanda a cikin shi ta bayyana rikita-rikitar da ta kai ga cire ta daga shugabancin hukumar a shekara ta 2021.

Tsohuwar shugabar Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen
Ruwa ta Nijeriya Hadiza Bala Usman ta fitar da wani littafi da
ta wallafa, wanda a cikin shi ta bayyana rikita-rikitar da ta kai
ga cire ta daga shugabancin hukumar a shekara ta 2021.

A cikin littafin, Hadiza Bala ta zargi tsohon Ministan Sufuri Rotimi Amaechi da kitsa silar cire ta daga aiki, saboda kawai ta ƙi riƙa yi ma shi ihisani da alfarmar da bai cancanta ba bisa ƙa’ida.

An dai dakatar da Hadiza ne tun cikin watan Mayu na shekara ta 2021, saboda Amaechi ya yi zargin ta kasa zuba kuɗaɗen harajin tashoshin jiragen ruwa Naira biliyan 165 a Asusun Tara Harajin Gwamnatin Tarayya.

Hadiza Bala ta ce Ameachi ya ce ba ya son aiki da ita a hukumar NPA, don haka ko dai ta kama gaban ta ko kuma ta je kotu kawai ta ƙalubalanci dakatarwar da ya yi mata.

Akwai dai zarge-zarge da dama a kan Amaechi cikin littafin, wanda a na shi ɓangaren ya ce idan ya kammala karanta shi kakaf zai maida martani dalla-dalla.

Leave a Reply