Home Labaru Daga Yanzu Duk Wanda Zai Shiga Fadar Shugaban Kasa Sai Ya Yi...

Daga Yanzu Duk Wanda Zai Shiga Fadar Shugaban Kasa Sai Ya Yi Gwaji

395
0

Daga yanzu masu kai ziyara Fadar Shugaban Najeriya sai sun yi rigakafin korona kafin a ba su damar shiga fadar mulkin ta Aso Rock Villa da ke Abuja.

A cewar mai magana da yawun shugaban ƙasa, Garba Shehu, wajibi ne a yi wa duk mai ziyara gwajin a kyauta a bakin ƙofa.

Cikin waɗanda dokar ta shafa har da gwamnoni da sauran manyan ƙasa ba waɗanda za su ga shugaban ƙasa ba kawai.

Sai dai ya ce akwai wasu shugabannin ƙasar waje ba lallai sai an yi musu “duk da cea su ma ana ba su shawarar su yi gwajin”, in ji shi.

Kyauta ake yin gwajin saboda haka babu wanda zai biya ko ƙwandala…duk wani mai ziyara, ba masu ganin shugaban ƙasa kaɗai ba, dole ne ya yi gwajin gaggawa a bakin ƙofa.”

LEAVE A REPLY