Home Labaru Da Umarnin Kotu Muka Kwashe Motoci Daga Gidan Matawalle – Gwamnatin Zamfara

Da Umarnin Kotu Muka Kwashe Motoci Daga Gidan Matawalle – Gwamnatin Zamfara

80
0

Gwamnatin jihar Zamfara, ta ce da umarnin Kotu aka kai
samame tare da kwashe motoci 40 a gidan tsohon gwamnan
jihar Muhammed Bello Matawalle.

Idan dai ba a manta ba, Bello Matawalle ya yi zargin cewa baya ga kwashe motocin sa na hawa, an kuma wawushe ɗakunan matan sa tare da zargin cewa Gwamna Dauda Lawal ne ya jagoranci samamen.

Sai dai babban mai ba gwamnan jihar Zamfara shawara a kan harkokin yada labarai Mustapha Jafaru Kaura, ya ce jami’an tsaro ne su ka kai samamen a gidan Matawalle bayan sun samu umarnin kotu.

Gwamnatin jihar Zamfara, ta ce duk motocin da aka dauko daga gidan tsohon gwamnan na gwamnatin ne, sannan ta karyata zargin da Matawalle ya yi cewa an dauki motoci masu dauke da hoton shi da shugaba Bpla Ahmed Tinubu.

Leave a Reply