Hukumar kula da harkokin sadarwa ta Nijeriya NCC, ta nanata cewa babu wani shirin kara kudin kiran wayar tarho sakamakon cire tallafin Man fetur da aka yi.
Babban mataimakin shugaban hukumar Farfesa Umar Garba Danbatta ya bada wannan tabbacin, yayin da ya ke karbar lambar yabon Titans of Tech a jihar Legas.
Ya ce hukumar NCC ba ta shirya kara kudin kiran waya a yanzu ba sakamakon cire tallafin Mai, sai dai ya rage ga dukkan kamfanonin sadarwa su duba abin da za su yanke.
Dambatta, wanda ya samu wakilcin shugaban hukumar na shiyyar Legas Mr Yomi Arowosafe, ya gode wa kamfanin da ya shirya lambar yabon tare da zakule shi har aka karrama shi, lamarin da ya bayyana a matsayin matakin da zai kara ma shi azama a fagen aiki.