Home Labaru Kasuwanci CBN Ya Sayar Wa Ƴan Canji Dala A Kan Naira Dubu 1...

CBN Ya Sayar Wa Ƴan Canji Dala A Kan Naira Dubu 1 Da 450

362
0
cbn2
cbn2

Babban Bankin Najeriya CBN ya fara sayar da dala ɗaya a kan N1,450 ga ƴan canji masu lasisi a ƙasa.

Babban Bankin ya sanar da matakin ne cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis,

wanda ake ganin matakin zai samar da wadatar dala a Najeriya wanda kuma zai sa farashin ta ya sauka a kan Naira.

Ɗaya daga cikin shugabannin ƴan kasuwar ƴancin ya shaida wa manema labarai cewa a ranar Alhamis an yi cinikin dala kusan 1,630,

amma bayan sanar da matakin farashin ta ya fara sauka

Babban Bankin ya buƙaci ƴan canjin su saka kuɗi a bankin domin samun dalar cikin farashin mai sauƙi tare da umartar su sayar da sauƙi a kasuwa.

Leave a Reply