Home Labaru Canada Da Hong Kong Sun Gano Wadanda Suka Kamu Da Nau’In Korona...

Canada Da Hong Kong Sun Gano Wadanda Suka Kamu Da Nau’In Korona Na Omicron

59
0

Kasar Kanada ta sanar da gano mutanen farko da suka kamu da cutar korona nau’in Omicron su biyu, da suka dawo balaguro daga Najeriya.

Gwamnatin Ontario, ta tabbatar da cewa mutanen biyu su na babban birnin kasar Ottawa.

Kawo yanzu an killace dukkan mutanen biyu a cibiyar killace masu fama da cutar korona da ke kasar, da kuma kokarin gano wadanda sukai mu’amala da su, kamar yadda jami’an kasar suka bayyana.

Ministan lafiyar Canada Jean-Yves Duclos, ya shaidawa manema labarai cewa an yi nasarar gano masu cutar ne a daidai lokacin da suka sauka a tashar jirgin sama.

A wani labara makamancin wannan da gidan talbijin na CTV na Hong kong ya rawaito, ya tabbatar da samun wasu mutum biyu da nau’in koronar na Omicron, wadanda suka dawo daga kasar Kanada.

Ma’aikatar lafiya da cibiyar dakike cutuka masu yaduwa na kasar da suka bayyana, sun ce babu tabbacin ko matafiyan ‘yan asalin Kanada ne, amma dai sun shiga kasar ne daga can.

Tun da fari jami’an lafiya sun ce matafiyan sun dauki cutar ne daga wani matafiyi, da ya dawo daga kasar Afirka ta Kudu, su na kuma zama a Otal guda. An dai killace bakin da suke Otal din, za kuma ayi musu gwaji domin tabbatar da ba sa dauke da sabon nau’in koronar mai saurin yaduwa.