Home Labaru CAF Ta Sahale Rike ‘Yan Wasan Afrika A Kungiyoyin Su Zuwa 3...

CAF Ta Sahale Rike ‘Yan Wasan Afrika A Kungiyoyin Su Zuwa 3 Ga Janairu 2022

50
0

Hukumar kwallon kafar Afrika CAF ta ce, ‘yan wasan nahiyar za su iya ci gaba da takawa kungiyoyin su leda har zuwa nan da ranar 3 ga watan Janairu gabanin komawa kasashen su don fara shirin tunkarar wasannin cin kofin nahiyar Afirka na bana.

Bisa hukuncin FIFA dai daga yau 27 ga watan Disamba ne, ya dace kungiyoyi su saki ‘yan wasan na nahiyar Afrika don fara shirye-shiryen gasar wadda za ta faro daga ranar 9 ga watan na Janairu.

Sai dai wata wasika da FIFA ta aikewa kungiyoyi ta bayyana musu cewa CAF ta amince da ba ‘yan wasan nahiyar damar ci gaba da taka leda har zuwa ranar 3 ga watan Janairu gabanin basu damar tafiya gida.

FIFA wadda ta bayyana matakin na CAF a matsayin girmamawa ga kungiyoyi wadanda yanzu haka ke fuskantar kalubalen sakin ‘yan wasan saboda asarar da hakan za ta haifar musu, bayan tattara karfin su wajen dogaro da ‘yan wasa Afrikawa.

Matakin CAF na nuna cewa yanzu Liverpool na da damar amfani da Mohamed Salah, da Sadio Mane, da kuma Naby Keita, a was an ta na ranar 2 ga watan Janairu da za ta kara da Chelsea wadda ita ma ke da damar amfani da mai tsaron ragar ta dan Senegal Edouard Mendy.

Gasar ta cin kofin Afrika da za ta gudana daga ranar 9 ga Janairu zuwa 6 ga Fabarairu na nuna cewa kungiyoyin firimiya ne kan gaba ta fuskar asarar ‘yan wasa da za su taka leda a gasar wanda ya shafi kusan dukkanin su, in banda Leeds United, da Newcastle United, da Norwich City da kuma Tottenham wadanda basu da asara.