Home Labaru Burkina Faso: Sojoji Sun Sanar Da Kwace Mulki

Burkina Faso: Sojoji Sun Sanar Da Kwace Mulki

142
0

Sojoji a Burkina Faso sun sanar da kwace mulki a kasar da ke yammacin Afirka, bayan boren da wani gungu daga cikinsu ya jagoranta kan yadda shugaban kasar ya kasa shawo kan matsalar hare-haren ta’addancin mayaka masu ikirarin jihadi.

Wani karamin jami’in soja ne ya sanar da dakatar da kundin tsarin mulkin kasar, da rusa gwamnati da majalisar dokokin kasar, da kuma rufe iyakokin kasar daga tsakar dare.

Kyaftin Sidsoré Kader Ouedraogo, ya ce sabuwar kungiyarsu ta sojoji ‘yan kishin kasa mai suna, ‘MPSR’ a takaice,  za ta sake kafa tsarin tsarin mulki a cikin lokacin da ya dace, inda ya kara da cewa za a kafa dokar hana fitar dare a fadin kasar.

A ranar Litinin ne dai manyan kasashen Afirka da na yammacin Turai suka yi tir da abinda suka kira yunkurin juyin mulki, yayin da kuma kungiyar EU ta bukaci a gaggauta sakin shugaba Roch Marc Christian Kabore da sojoji suka kama.

Amurka ta kuma yi kira da a saki Kabore tare da yin kira ga jami’an tsaro da su mutunta kundin tsarin mulkin Burkina Faso da shugabancin farar hula.

Shi ma dai Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres cikin sanarwar da ya fitar, yayi tir ne da yunkurin kwace gwamnati da karfin tsiya, matakin da ya bayyana a matsayin juyin mulki.