Home Labaru Buhari Ya Tura Sunan Wanda Ya Ke So A Ba Minista Daga...

Buhari Ya Tura Sunan Wanda Ya Ke So A Ba Minista Daga Jihar Katsina

298
0

Rahotanni na, cewa tsohon shugaban kasa Muhammadu
Buhari ya tura sunan wanda ya kamata shugaba Tinubu ya
nada a matsayin minista daga jihar Katsina.

Ana dai bukatar Tinubu ya nada minista daga kowace jiha da kuma babban birnin tarayya Abuja, domin taimaka masa wajen tafiyar da gwamnatin Nijeriya.

Wata majiya ta ce, shugaba Tinubu ya karrama Buhari ta hanyar ba shi damar gabatar da wanda ya ke so a ba kujerar minista daga jihar Katsina.

Majiyar ta kara da cewa, tuni tsohon shugaban kasa Buhari ya girmama karramawar, kuma an ce ya aike da sunan wani ga shugaba Tinubu, sai dai har yanzu ba a samu labarin wanda aka ce shi ne Buhari ya mika sunan sa ba.

Leave a Reply