Home Labarai Buhari Ya Sha Kaye A Kotun Koli A Shari’a Kan Dokar Zabe Ta 2022

Buhari Ya Sha Kaye A Kotun Koli A Shari’a Kan Dokar Zabe Ta 2022

113
0

Kotun Koli ta yi watsi da karar da Shugaba Buhari da Babban
lauyan gwamnatin tarayya su ka shigar, inda su ka bukaci fashin
baki a kan sashe na 84 na dokar zabe ta shekara ta 2022 da aka
yi wa garambawul.

Sashen dai ya haramata wa duk wani mai rike da mukamin siyasa da aka nada a dukkan matakai ya kada kuri’a a zaben fidda gwani na duk wata jam’iyya.

Alkalan Kotun bakwai a karkashin jagorancin Mai Shari’a Musa Dattijo, dukan su sun amince cewa karar yunkurin wahalar da kotu ne kawai.

A hukuncin da Mai Shari’a Akomaye Agi ya karanto, Kotun Kolin ta ce ba zai yiwu Shugaba Buhari ya nemi a goge sashen na 84 bayan a baya ya aminta da shi.

Ya ce Shugaban kasa ba ya da ikon bukatar majalisa ko tursasa ta ta sauya wani abu a dokar da a baya ya bada hadin kai ya kuma aminta da ita.